Kungiyar Izala tace ba koyarwar musulunci bane kirawa shugaba mutuwa

Kungiyar Izala tace ba koyarwar musulunci bane kirawa shugaba mutuwa

– Kungiyar Izala tace masu yada jita-jitar cewa shugaba Buhari yam utu jahilai ne

– Kungiyar tace kirawa shugaban mutuwa rashin imani ne da tausayi

– Sheikh Sani Jingir yace kamar kowa Buhari zai rasu wata rana

Kungiyar Izala tace ba koyarwar musulunci bane kirawa shugaba mutuwa

Kungiyar Izala tace ba koyarwar musulunci bane kirawa shugaba mutuwa

Kungiyar nan ta Izalatul Bidi’a wa Iqamatus Sunnah ta Kasa ta soki masu kirawa shugaba Buhari mutuwa. Kungiyar tace hakan ba komai ba ne sai zallan jahilci da rashin imani da tausayi.

Shugaban Majalisar Malamai na Kasa na Kungiyar Sheikh Sani Yahaya Jingir yace masu kiran shugaban kasar ya mutu, mutane marasa gaskiya da suka aikata ba daidai ba. Sheikh Jingir yace wata rana kamar kowa shugaba Buhari zai bar Duniya kamar yadda kowa zai bar ta.

KU KARANTA: Za a binciki Mukaddashin shugaban Kasa

Shehun Malamin yayi kira da Gwamnati ta sayi kayan gona ta rika saidawa talakawa cikin rahusa, Yace wannan zai rage radadin da ake fama da shin a yunwa da rashin kudi a fadin Kasar. A karshe Malamin ya soki kalaman Faston nan da yace a kashe Fulani, yace hakan na iya tada fitina.

Mun samu labari har wa yau daga Jaridar Daily Trust cewa wani matashi ya rataye kan sa har Lahira a Garin Kano. Har yanzu dai ba za a iya cewa ga dalilin da ya sa wannan matashi ya aikata wannan mugun abu ba.

Shugaban kungiyar Izala ya bayyana wanda tsokaicin Fasto Johnson Suleman kan Fulani makiyaya zai yiwu kawo rikici.

“Kowane shugaban adddini, Musulmai ne ko Kiristoci da yayi maganar wuta, Shi, ba shugaba bane. Saboda haka, yakamata duk shugaban addinai su tunani kafin suke yi magana. Kuma su yi wa’azi kan zaman lafiyar yan Najeriya,” yace.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel