‘Yan iskan Gari sun kai hari ga tawagar Gwamna

‘Yan iskan Gari sun kai hari ga tawagar Gwamna

– Wasu ‘Yan iskan Garin sun kai wa Gwamna Mimiko hari

– ‘Yan iskan sun kai harin ne ga tawagar Gwamnan

– Sun dai hana Mai Girma Gwamnan zuwa Majalisa

‘Yan iskan Gari sun kai hari ga tawagar Gwamna

‘Yan iskan Gari sun kai hari ga tawagar Gwamna

Wasu ‘yan iskan Gari sun kai hari ga tawagar motocin Gwamnan Jihar Ondo Olusegun Mimiko. Wadannan ‘Yan iska dai sun yi barna ga motoci biyu da ke cikin tawagar.

Wannan abu dai ya faru ne yayin da Gwamnan ke kokarin zuwa Majalisar Jihar domin ya bayyana kasafin kudin wannan shekarar. Mazauna Yankin dai sun san yadda suka yi, suka hana Gwamnan da tawagar sa wucewa.

KU KARANTA: An juyawa Najeriya baya inji Shehu Sani

Hukumar dillacin labarai na Kasa watau NAN tace rikicin yayi kamari, don haka dole Gwamnan ya fasa zuwa inda yayi niyya. A karshe dai mutane da dama sun samu rauni don aran-gamar da suka yi da Jami’an tsaro. Sai dai mutanen sun ce zanga-zangar su ke yi ba tada rikici ba, su na mai kokawa da halin ‘Yan Sandan.

A can Jihar Kaduna kuma, Hukumar ‘Yan Sanda ta samu nasarar damke wasu daga cikin masu hannu a rikicin Kudancin Kaduna. ‘Yan Sanda dai sun kama mutane 17 da manyan makamai guda 29. Za a gurfanar da wadannan mutane a Gaban Kotu.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel