Kasashen Afirka ta juya wa Najeriya baya - Inji Sanata Sani

Kasashen Afirka ta juya wa Najeriya baya - Inji Sanata Sani

Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya ce kasar Najeriya tunbin giwa ne kawai saboda ta daina samu goyon bayan saurar kasashen Afrika.

Kasashen Afirka

Sanata Shehu Sani

Sanata Shehu Sani ya ce kasashen Afrika ta daina neman jagorancin kasar Najeriya duk da rawar da ta taka a ceton kasar Gambia daga juyin siyasa.

Dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanatan Shehu Sani ya yi wannan furujin ne a ranar Laraba, 1 ga watan Fabrairu, a cikin wani gajeren bayani.

A cewar dan majalisar, wannan al’amari na shedar yanda kasa Najeriya ta rasa duk kujeru a zaben kungiyar tarayyar Afirka a wata ganawarsa a hedkwata a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Moussa Mahamat na Chadi ya lashe kujeran sabon shugaban kungiyar tarayyar Afirka a inda sauran yan takara da Najeriya suka sha kashi.

Sani ya sa laifin a kan kasar Najeriya saboda rashin isashen shiri kafin zaben kuma ya ce Najeriya ta rasa goyon bayan saurar kasashen Afrika.

Sanatan ya yi kira ga gwamnati cewa dole ne mu gyara halayen mu. Wannan wata kira ne.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel