An bukaci gwamna El-Rufai ya janye dokar ta-ɓaci a garin Zangon Kataf

An bukaci gwamna El-Rufai ya janye dokar ta-ɓaci a garin Zangon Kataf

Al’ummar kudancin Kaduna dake karamar hukumar Zangon Kataf sun roki gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da yayi wa Allah yayi wa Annabi ya janye musu dokar ta-baci daya kakaba musu sakamakon hare haren kabilanci da suka yi fama da shi a kwanakin baya.

An bukaci gwamna El-Rufa'i ya janye dokar ta-ɓaci a garin Zangon Kataf

Gwamnatin jihar ta sanya dokar ta-bacin ne biyo bayan harin da aka kai a kasuwar Samarun Kataf a ranar 17 ga watan Janairu, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane uku.

KU KARANTA: PDP ta shiga halin talauci, ta gagara biyan albashin ma’aikatanta

Al’ummar yankin sun koka sosai dangane da dokar hana fitan, inda suka ce dokar ta sanya su cikin mawuyacin hali ta yadda basu da wani katabus na gudanar da kasuwancisu, kuma makarantu ma a kulle suke.

Wani mazaunin unguwar Madakiya a karamar humar Zangon Kataf Abba Woje ya nuna damuwarsa game da dokar ta bacin kamar haka “saboda wannan dokar, ba’a bude bankuna, kasuwanni ma a rufe suke, yara ma basa zuwa makaranta.”

Daga karshe sai ya roki gwamnatin jihar Kaduna data sassauta musu dokar, ko zasu samu saukin rayuwa da walwala.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel