Jami’in dan sanda ya kashe matarsa sannan ya harbe kansa a Uganda, inda suka bar yara uku (hotuna)

Jami’in dan sanda ya kashe matarsa sannan ya harbe kansa a Uganda, inda suka bar yara uku (hotuna)

A ranar Alhamis, 2 ga watan Fabrairu, an rahoto cewa wani dan sanda ya harbe matarsa har lahira, bayan nan ya juya bindigar shima ya kashe kansa a barikin yan sandan Nsambya, kasar Uganda.

Jami’in dan sanda ya kashe matarsa sannan ya harbe kansa a Uganda, inda suka bar yara uku (hotuna)

Marigayiya Esther Caroline

A cewar wani da abun ya faru a kan idannunta, makwabta sun shiga rudani da suka ji harbin farko. Sun kara da cewa, lokacin da ta koma don duba abunda ya faru, taga jinni na kwaranya sannan ta kuma jin karan harbi na biyu, a wannan lokacin ne ya nemi doki sannan ta gudu.

“Na shawarci sauran makwabta da cewa karda su shiga gurin, sannan muka jira har saida yan sanda suka zo,” cewar idon shaida.

KU KARANTA KUMA: An kama wani mutumi yana marin gawan mamaci a lokacin jana’iza (hoto/bidiyo)

Jami’in dan sanda ya kashe matarsa sannan ya harbe kansa a Uganda, inda suka bar yara uku (hotuna)

'Yayansu guda uku

A halin yanzu, majiyar yan sanda a Nsambya, sun bayyana mana cewa an dawo da Sabitii wanda ya fito daga yankin Alur, Mbarara. A halin yanzu, Sabiiti yayi aiki a hukumar yan sanda tsawon shekaru 12.

Har yanzu ba’a san abunda ya faru a tsakaninsa da matarsa ba cikin dare wanda ya kais hi ga harbe ta da kuma harbe kansa. Haka kuma, an kai gawarsu dakin ajiye gawa na birnin garin don bincike.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016-
2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016- 2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel