Yan Najeriya miliyan 135 ne ke amfani da wayan Salula

Yan Najeriya miliyan 135 ne ke amfani da wayan Salula

Hukumar fitar da alkalumma ta kasa (NBS) ta bayyana cewar yan Najeriya su miliyan 35 ne ke amfani da wayar Salula a cikin shekaru 11 da suka gabata.

Yan Najeriya miliyan 135 ne ke amfani da wayan Salula

Yan Najeriya miliyan 135 ne ke amfani da wayan Salula

Hukumar NBS ta bayyana haka ne a Abuja, inda tace yawan masu amfani da wayar tafi da gidanka ya karu da miliyan 5,443,240 daga karshen shekarar 2015 zuwa farkon shekarar 2016. Rahoton ya bayyana cewar bangaren kimiyyar waya ta samar ma Najeriya yawan kudade da suka kai naira tiriliyan 1.40 a kashi na uku na shekarar 2016.

KU KARANTA: Kungiyar Izala ta dauki nauyin karatun marayu 21 a Bauchi

Haka zalika bincike ya nuna cewar kamfanin waya na Airtel tafi samun karin masu cinikayya dasu, inda masu amfani da layin suka karu daga miliyan 32.78 zuwa miliyan 34.12, yayin da kuma Etisalat ta zamto layin da tafi asarar abokan cinikayya, inda masu amfani da layin suka ragu daga miliyan 22.54 zuwa miliyan 20.81.

Yayin da kamfanin Glo keda yawan abokan cinikayya har miliyan 37.36, sai MTN kuma dake da abokan hulda su miliyan 61.84.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel