PDP ta shiga halin talauci, ta gagara biyan albashin ma’aikatanta

PDP ta shiga halin talauci, ta gagara biyan albashin ma’aikatanta

Bincike ya nuna cewar jam’iyyar PDP bangaren Ahmed Makarfi na cikin halin tsaka mai wuya, yayin da rashin kudaden shiga ya dabaibayeta, inda har ma zata kulle cibiyar tsare tsaren ta.

Majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun tsegunta mana cewar PDP bangaren Makarfi ta gaza wajen biyan albashin ma’aikatanta kusan watanni uku da suka gabata, kuma ta daina biyan yan kwangila wadanda ta sanya gudanar da aikace aikace daban daban.

PDP ta shiga halin talauci, ta gagara biyan albashin ma’aikatanta

Sai dai Kaakakin jam’iyyar a bangaren Makarfi ya Prince Dayo Adeyeye ya musanta batun, inda ya bayyana ma jaridar LEADERSHIP cewar jam’iyyar bata taba fashin sauke nauyinta da suka shafi kudi ba tun bayan shan kayin da tayi a zabukan 2015.

Ita ma kungiyar ma’aikatan jam’iyyar PDP ta musanta batun, inda tace sama da kaso 70 na yayan kungiyar sun samu albashinsu na watan Janairu a jiya.

KU KARANTA: Abinci wani, guban wani: PDP tayi asarar Andy Uba, ya cafki APC

Bincike ya nuna cewar tun bayan faduwa zabukan 2015 ne jam’iyyar PDP ta shiga halin fatara da talauci, mun samu wannan labara ne daga wata majiya mai tushe ta cikin jam’iyyar wanda tace “idan zaku iya tunawa tun bayan da wa’adin mulkin majalisar zartarwar jam’iyyar data gaba ya kare, sun shaida cewar akwai kimanin sauran naira miliyan 350 a asusun jam’iyyar, daga cikin naira biliyan 13 da suka ce sun tara ma jam’yyar don yakin neman zaben Goodluck Jonathan.

“Tun bayan wannan lokacin ne jam’iyyar ta shiga halin rashin kudi, kuma wannan ya kawo rarrabuwar kawuna tsakanin yayan jam’iyyar. Sai dai akwai rade radin cewar shugaban dayan tsagen jam’iyyar Ali Modu Sheriff yayi ma jam’iyyar tayin biyan kudin hayan gidan da cibiyar tsare tsaren jam’yyar take zaune, tare da biyan albashin ma’aikatan.''

Majiyar ta kara da cewa “albashin da ake biyan ma’aikatan jam’iyyar PDP ya kai N18m, kuma sun kasa biya tun watan Yulin bara, da alama kuma ba zasu iya biya ba har sai an magance matsalar shugabanci data addabi jam’iyyar. A yanzu haka wasu shuwagabannin jam’iyyar APC sun fara yi ma wasu manyan jami’an jam’iyyar PDP tayin shigowa jam’iyyarsu don suna ganin zasu yi ma jam’iyyarsu amfani, tare da kara karya alkadarin PDP.''

Majiyar ta shaida mana Makarfi baya shiri da yawancin gwamnonin jam’iyyar, hakan ya sanya Makarfi goyon bayan kasancewar gwamna Ayo Fayose a matsayin shugaban gwamnonin jam’iyyar, don ya samu ya biya basussukan da ake bin jam’iyyar.

A nan ma Kaakakin jam’iyyar, Dayo ya musanta batun tsatstsamar alaka tsakanin Makarfi da gwamnonin jam’iyyar, inda yace “karya ne kawai, kuma Makarfi nada alaka kyakkyawa tsakninsa da gwamnonin jam’iyyarmu, sakamakon shima tsohon gwamna ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel