Munyi alkawarin canji kuma yazo – Lai Mohammed

Munyi alkawarin canji kuma yazo – Lai Mohammed

- Ministan bayanai da al’adu Lai Mohammed yace jam’iyya mai ci bata shirya ma yawan ta’adi da tarar a mulki ba

- Ministan ya kara da cewa ‘canjin’ da jam’iyya mai ci tayi alkawari ya fara bayyana

- A cewarsa, akwai canji daga rashin hukunci zuwa gaskiya

Munyi alkawarin canji kuma yazo – Lai Mohammed

Lai Mohammed yace basu san barnan da akayi ya kai haka ba a lokacin da suka karbi mulki

Ministan bayanai da al’adun Najeriya Lai Mohammed ya yarda da cewan jam’iyya mai ci ta mamaye matakin hauka, rashin da’a da kuma rashin adalci a Najeriya.

A cewar sa, jam’iyyar bata shirya ma yawan ta’adi da ta tarar ba a lokacin da ta karba mulki daga hannun gwamnatin dake a kasa a 2015.

Sannan yayi ikirarin cewa canjin da gwamnati mai ci tayi way an Najeriya alkawari ya fara bayyana.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya jagoranci taron majalisa a bayan Buhari

Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da jaridar Sun a kwanan nan.

Yace: “Bari muyi duba cikin al’amarin, na daya, munyi alkawarin canji kuma wannan canjin yazo. Akwai canji a yau daga rashin gaskiya zuwa ci gaba kuma wannan na nufin abubuwa da dama. A yau akwai canji daga cin hanci da rashawa zuwa aminci, wannan na nufin abubuwa da dama.

“Akwai canji a yau kan yadda mutane ke kallon cin hanci da rashawa fiye da yadda ake duban sa a da. Babu rayuwar nuna kai a yanzu. A shekarar 2014 lokacin da tsohon shugaban kasa yaje Kenya, kimanin jiragen sama 100 na suka take mai baya.”

Da yaci gaba da bayani, ya nace kan cewa lallai jam’iyyar bata san yawan ta’adi da kasar ke ciki ba.

“Abunda bamu sani ba shine matakin barna da kazanta, matakin kazanta da rashawa shine abunda bamu sani ba. Mun san cewa abubuwa sun lalace amma bamu san lalacin ya kai haka ba. Bamu san cewa kafin mu shigo babu kudi ko kadan ba."

A halin yanzu, shahararen mawakin nan Tuface Idibia zai jagoranci zanga-zangar kasa baki daya a kan gwamnatin tarayya sakamakon halin da tattalin arkizin kasar ke ciki.

Ana sa ran zanga-zangar da za’ayi a ranar 6 ga watan Fabrairu zai janyo hankulan matasan Najeriya da dama wadanda basu ji dadin gwamnati mai ci a yanzu.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel