Kotu ta daure wani soja shekara 7 a gidan yari

Kotu ta daure wani soja shekara 7 a gidan yari

Kotun musamman ta rundunar sojin Najeriya da ke zamanta a Maiduguri, babban birnin jihar Borno ta yanke wa wani sojan kasar zaman gida yari na shekara 7, bayan samunsa da laifin kisa ba da niyya ba.

Kotu ta daure wani soja shekara 7 a gidan yari

Kotu ta daure wani soja shekara 7 a gidan yari

Sojan wanda ba a bayyana sunansa ba kotun ta musamman ta same shi da laifin harbe wani mutum, mai suna Umar Alkali a kasuwar Monday Market da ke Maiduguri a ranar 23 ga watan Disamba na shekara ta 2015.

Kotun ta ki amincewa da hujjar da sojan ya gabatar ta cewa ya harbi mutumin ne a kokarin kare kansa.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun kwato makamai, motoci bayan arangama da yan Boko Haram

Inda ya ce mutumin ya yi kokarin kwace bindigarsa ne, wanda a kan haka ne shi kuma ya harbe mutumin.

Sanarwar da kakakin rundunar sojin Birgediya Janar Sani Usman Kuka-sheka ya bayar mai dauke da bayanin, ta kuma ce kotun, wadda ke karkashin shugabancin Birgediya Janar Olusegun Adeniyi, ta kuma sami wani sojan da laifin guje wa aikin soji, wanda ta yanke masa hukuncin daurin wata 14.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel