Kotun soji ta jefa soja kurkuku akan laifin tserewa Boko Haram

Kotun soji ta jefa soja kurkuku akan laifin tserewa Boko Haram

Wata kotun soji ta yankewa wani sojan Najeriya mai suna, Egbechi Oze, hukuncin kurkuku a Maiduguri,jihar Borno bayan ya gudu daga aiki.

Kotun soji ta jefa soja kurkuku akan laifin tserewa Boko Haram

Kotun soji ta jefa soja kurkuku akan laifin tserewa Boko Haram

Jaridar Premium Times ta bada rahoton cewa ya gudu daga aikin tsawon kwanaki 270 inda ya tserewa Boko Haram ya buya a wani jiha a yankin kudu maso gabas.

Sojan na daya daga cikin wadanda ake kirgawa cewa sun bace bayan mayakan Boko Haram sun kai hari barikin soji a Gwoza.

KU KARANTA: Boko haram ta kashe soji 3

Kotun tace duk da cewa Oze ya bar aikinsa na kusan shekara daya, zai cigaba da amfana da hakkinsa.

An tuhumesa da laifin rashin lissafin makami da hasasai da ya amsa a lokacin harin amma daga bayan an wanke sa.

Dalilan wannan shine ya rasa makaman bayan yan Boko Haram sun dake shi kafin soji suka kai hari wurin.

An yanke masa hukunci watanni 14 a gidan yari kuma kotun tace ya yiwuwar a koreshi daga gidan soja.

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel