HALIN BERA: Tsohon minista ya yi alkawarin dawo da miliyan 417

HALIN BERA: Tsohon minista ya yi alkawarin dawo da miliyan 417

- Tsohon ministan tsaro Musiliu Obanikoro ya dawo da wasu kudi naira miliyan 30 ga jami’in hukumar Laifuka da Tattalin Arziki.

- Saidai kuma ya yi alkawarin dawo da wasu makudan kudi naira miliyan 417 a nan gaba.

HALIN BERA

Sanata Musiliu Obanikoro

Tsohon karamar ministan tsaro Sanata Musiliu Obanikoro ya dawo da wasu karin kudi naira miliyan 30 ga jami’in hukumar Laifuka da Tattalin Arzikin kasa (EFCC).

Jaridar Punch ta rahoto cewa ministan ya kuma yin alkawarin maida wasu kudi naira miliyan 417 a nan gaba.

KU KARANTA KUMA: An koro ‘Yan Najeriya daga Turai

Lissafi ta nuna cewa tsohon ministan yanzu atakace ya mayar da kudi naira miliyan 167 ga ajihun gwamnatin tarayya.

Wata kwakwarar majiya ta shaida wa manema labarai cewa tsohon ministan ya bayar da wannan kudin ne daga asusunsa na Diamond Bank zuwa ga asusun EFCC.

Majiyar ta bayyana cewa Sanata Obanikoro ya cika wata ɓangare na yarjejeniya da ya yi da hukumar. Za ku iya tuna cewa a bara, tsohon ministan ya yi alkawarin mayar da wasu adadin kudi kowane kwatan sabuwar shekara.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018
NAIJ.com
Mailfire view pixel