Abinci wani, guban wani: PDP tayi asarar Andy Uba, ya cafki APC

Abinci wani, guban wani: PDP tayi asarar Andy Uba, ya cafki APC

Sanata mai wakiltar al’ummar mazabar Anambra ta kudu, Sanata Andy Uba ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki daga jam’iyyar PDP.

Abinci wani, guban wani: PDP tayi asarar Andy Uba, ya cafki APC

Andy Uba ya bayyana canjin shekar nasa ne a ranar Laraba a can kauyensa na Uga dake karamar hukumar Aguata na jihar Anambra, inda yace ya gane cewar manufar jam’iyyar APC yayi daidai da manufarsa na samar ma jama’ansa ingantaccen wakilanci.

KU KARANTA: ‘Matukar ina raye, ba zan daina ɓaɓatu ba’ – Shehu Sani

Uba ya kara da cewar ya shiga jam’iyyar APC ne sakamakon irin jiga jigan jam’iyyar dake cikinta, wadanda yake koyi dasu kamar su Sanata Ngige da Cif George Moghalu, inda yace ire iren jigajigan yan siyasan nan zasu kai jam’iyyar ga samun nasarori.

Daga karshe Sanata Andy Uba ya tabbatar ma al’ummar mazabansa zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya kyautata musu, sa’annan yayi kira ga yan kabilar Ibo dasu shigo jam’iyyar kwansu da kwarkwata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel