Kungiyar Izala ta dauki nauyin karatun marayu 21 a Bauchi

Kungiyar Izala ta dauki nauyin karatun marayu 21 a Bauchi

Kwamitin masallacin Gwallaga dake kula da marayu da gajiyayyu na kingiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) reshen jihar Bauchi ta dauki nauyin karatun yara marayu su 17, sa’annan ta tura wasu guda 4 makarantar koyan sana’a.

Kungiyar Izala ta dauki nauyin karatun marayu 21a Bauchi

Kungiyar Izala ta dauki nauyin karatun marayu 21a Bauchi

Sakataren kwamitin, Alhaji Usamatu Mohammed ne ya bayyana haka a wata hira da yayi da manema labarai yayin kaddamar da shirin daukan nauyin marayu a masallacin Gwallaga dake jihar Bauchi.

KU KARANTA: ‘Matukar ina raye, ba zan daina ɓaɓatu ba’ – Shehu Sani

Alhaji Usamatu yace kungiyar izala zata dauki nauyin karatun yaran tun daga Firamari har Sakandari, sa’annan ya kara da cewa kungiyar zata dinga biyan masu rike da yaran kudin kula da dawainiyarsu a duk wata, inda kuma za’a baiwa masu koyar sana’a kudin mota da kayan aiki.

Usamatu yace kwamitin nada tabbacin wannan tallafi zai yi amfani matuka ga iyalan wadanda abin ya shafa, tare da rage musu radadin talauci, inda ya kara da cewa akwai wasu attajirai da suka dauki alkawarin daukan wasu marayu na daban, don basu ingantaccen ilimi.

Daga karshe yayi kira ga sauran attajirai da suyi koyi da ire iren kungiyoyin nan, don tallafa ma marayu da gajiyayyu. “wajibinmu ne mu lura da marayun cikin mu, suna bukatar mu kula dasu, wajibinmu ne mu taimake su wajen gina musu rayuwa mai kyau.” Inji shi.

A nasa jawabin, wani hakimi, Alhaji Nura Adamu Jumba yayi kira ga wadanda suka amfana da shirin da kada suyi wasa da wannan damar da suka samu, kuma su dage da karatu. Hakimin ya ja hankalin su dasu su sani ilimi shine gishirin zaman duniya.

Jumba ya karkare jawabinsa da shawartar masu rike da yaran dasu dage wajen ganin sun seta yaran tare da basu kulawa don su zamto yan kasa na gari, wadanda zasu amfanar da al’ummarsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel