Gwamnatin tarayya ta kafa hukuma kan duba hauhawar farashin kayan abinci

Gwamnatin tarayya ta kafa hukuma kan duba hauhawar farashin kayan abinci

Gwamnatin tarayya ta kafa wata hukuma akan duba hauhawar kayan abincin da ke faruwa a kasuwanni.

Gwamnatin tarayya ta kafa hukuma kan duba hauhawar farashin kayan abinci

Gwamnatin tarayya ta kafa hukuma kan duba hauhawar farashin kayan abinci

Ministan labarai da al’adu ,Alhaji Lai Mohammed, bayan taron majalisan zantarwa ne ya bayyana haka a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Minstan ya bayyana damuwarsa akan cewa kayan masarufi basu samun isa kasuwanni kuma idan akaci sa’a suka kai, ana sayarwa da tsawallallen farashi.

KU KARANTA: Dan sanda yayi ma mata jina-jina

Yace ana sa ran kwamitin zata kawo rahoton bincikenta a mako mai zuwa kuma za’a dau matakan da ya kamata akan hauhawar farashin kayan masarufin.

Mohammed yace: “Gwamnati ta damu da hauhawar farashin kayan abinci da kuma matsalan cewa yawancin lokuta, kayan masarufi basu samun daman shiga kasuwa kuma ana sayarwa a farashi mai tsada.

“Saboda haka, gwamnati ta nada wata hukuma akan tsaron kayan masarufi wanda zai tabbatar da dakile wannan asara da akeyi. Wannan kwamitin ta kunshi ministan akin noma,kudi, ruwa da sufuri.

“Abu mai muhimmanci shine a duba abinda gwamnati zata iya samarwa. Wannan tallafi zai iya zama a sashen sufurin mota, ana shirin haka kuma wannan na nuna cewa gwamnati ta damu da tashin kuin kayan masarufi.”

Wannan taron majalisan zantarwa dai ta gudana ne karkashin jagorancin mukaddashin shugaban kasa,Farfesa Yemi Osinbajo.

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018
NAIJ.com
Mailfire view pixel