Kotu ta yanke ma yaron tsohon minista Bala Mohammed zaman gidan yari

Kotu ta yanke ma yaron tsohon minista Bala Mohammed zaman gidan yari

Babban kotun birnin tarayya ta daure yaron tsohon minista Bala Mohammed, Shamsuddeen Bala Mohammed a jiya bayan ya gurfana gabanta kan tuhumarsa da ake yi da laifukan zamba da satar kudaden gwamnati.

Kotu ta yanke ma yaron tsohon minista Bala Mohammed zaman gidan yari

Mai shari’a Nnamdi Dimgba ne ya yanke hukuncin a jiya Laraba 1 ga watan Feburairu, inda ya bukaci a jibge Shamsuddeen a gidan yarin Kuje kafin kotu da duba yiwuwar bada belinsa a ranar Juma’a 3 ga watan Feburairu kamar yadda lauyansa ya bukata.

KU KARANTA: EFCC ta gurfanar da Minista da ɗansa gaban ƙuliya manta sabo

Lauyan hukumar EFCC, Prince Ben Ikani ya roki kotu da kada ta bada belin Shamsuddeen, sakamakon zai iya lalata tarin hujjojin da suke da shi akansa, lauyan yace Shamsuddeen yayi watsi da umarnin kotu a baya yayin da ta umarce shi daya mika wasu takardu ga hukumar EFCC bayan ta bada belinsa.

Kotu ta yanke ma yaron tsohon minista Bala Mohammed zaman gidan yari

Ana tuhumar Shamsuddeen da laifuka 15 da suka sahfi satar kudade, da kuma karya yayin bayyana kadarorinsa. Ana tuhumarsa ne tare da kamfanuwa guda 4 da suka hada da Bird Trust Agro Allied Limited, Intertrans Global Logisitics Ltd, Diakin Telecommunications Ltd da Bal-Vac Mining Nigeria Ltd.

Shima wani lauyan mai suna Chris Uche Ikani yace, tun da a baya an bada Shamsuddeen, amma ya gagara cika sharuddan beli, don haka ba mutumin da za’a aminta da shi bane.

Sai dai lauyan Shamsuddeen ya roki kotu data bada belin wanda ake zargin, inda yace Shamsuddeen bai mika ma EFCC fasfon sa bane saboda hukumar ta EFCC bata nema ba.

Daga karshe alkalin kotun ya daga sauraron karar zuwa 27 da 28 na watan Maris.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel