Birtaniya ta koro yan Najeriya 40 daga kasar ta

Birtaniya ta koro yan Najeriya 40 daga kasar ta

-A safiyar ranar Laraba ne dai wasu 'yan Nigeria kimanin 40 wadanda aka tasa keyarsu daga Birtaniya suka iso filin jirgin saman Lagos

-A cikin mutane 40 din wadanda hukumar shige da fice ta kasa ta tabbatar an dawo da su kasar, har da mata da tsofaffi da kuma fursunoni

Birtaniya ta koro yan Najeriya 40 daga kasar ta

Birtaniya ta koro yan Najeriya 40 daga kasar ta

Hukumar da ma wasu Jami'an tsaron Najeriya wadanda suka hada da 'yan sanda, sun halarci filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Lagao domin tarbar mutanen.

Wakilinmu da ke Lagos ya shaida mana cewa babu wani karin bayani da hukumomi suka yi game da laifukan da suka aikata.

Sai dai a cikinsu akwai wadanda suka fara zaman gidan kaso tun suna Birtaniyan kuma zasu ci gaba da zama a jarun har sai sun kammala wa'adin da aka dibar musu.

Mutanen da dama sun iso cikin wani irin mawuyacin hali inda wasu daga cikinsu suka nuna alamun galabaita.

A wani labarin kuma, Gwamnatin hadin gwiwar Austria ta amince ta hana mata saka burka a wurin taruwar jama'a kamar makarantu da kotuna.

Kasar tana kuma duba yiwuwar hana ma'aikatan kasar saka dankwali da wasu tufafi masu alaƙa da addini.

Ana ganin wannan shawara a matsayin wani yunƙurin daƙile 'yancin da jam'iyyar masu ra'ayin rikau, wanda dan takararsu ya sha kaye da kyar a zaben shugaban kasar na watan da ya gabata ke ci gaba da samu.

A makon da ya gabata ne gamayyar jam'iyyu masu matsakaicin ra'ayi suka kusa rugujewa sakamakon wani rikici a kan wata yarjejeniya game da makomar gwamnatin.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel