Mawaki 2face zai jagoranci zanga-zangar adawa da salon mulkin Buhari

Mawaki 2face zai jagoranci zanga-zangar adawa da salon mulkin Buhari

- Fitaccen mawakin Najeriya 2face Idibia ya yi kira ga masoyan shi su fito zanga-zanga a ranar Talatar makon gobe domin adawa da matsin tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya

- Zalika mawakin ya bukaci gwamnatin kasar da ta dauki matakan magance matsalar

Mawaki 2face zai jagoranci zanga-zangar adawa da salon mulkin Buhari

Mawaki 2face zai jagoranci zanga-zangar adawa da salon mulkin Buhari

2face ya yi kiran ne a wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafin shi na facebook, wanda kuma cikin sa’a guda, sama da mutane dubu ashirin da biyu suka kalli sakon.

Kafofin sadarwa na intanet dai sun kasance hanyoyin kiran gangamin zanga-zanga a Afrika, to sai dai kuma abin mamaki ne mawaki ya fito ya dauki irin wannan matsayin na siyasa.

A tataunawarsa da majiyar mu, mawakin Pop da ake kira DR Pure a Kano, ya ce ko da yake, suna goyon bayan kawo karshen matsin tattalin arziki da al’ummar Najeriya ke fuskanta, ba zanga zanga ba ce hanya mafi dacewa wajen jan hankalin gwamnati.

A cewar Dr Pure, kamata yayi mawaka su bi hanyoyin da suka dace, cikin ruwan sanyi gami da hikima, wajen bada gudunmawarsu domin samun sauki ga ‘yan Najeriya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel