Kungiyar 'yan na tsaya tare da Buhari za ta kaddamar da gangamin taro na kasa

Kungiyar 'yan na tsaya tare da Buhari za ta kaddamar da gangamin taro na kasa

Kungiyar goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da gangamin taron nuna adawa da shirin taron zanga-zanga na 5th da 6th a wannan watar.

Kungiyar 'yan na tsaya tare da Buhari

Kungiyar ‘yan "Na tsaya tare da Buhari" za ta kaddamar da wani gangamin a duk fadin Najeriya domin nuna rashin amincewar ta da gangamin taron da shararen mawaki 2baba Innocent Idibia zai jagoranta.

Kungiyar ta rubuta a shafin Fesbuk na ta cewa, za ta kaddamar da wannan gangamin ne ranar da shi mawakan zai gudanar da taron nuna adawa ga gwamnatin shugaba Buhari.

Rubutun na kamar haka: "#iStandWithBuhari” taron hadin gangami na kasa 5th & 6th ga watan Fabrairu, 2017.

KU KARANTA KUMA: Mulkin Buhari: Kura ta kai bango; Za a fara zanga-zanga

A halin yanzu, Mataimakin Shugaba Muhammadu Buhari na musamma a kan kafofin watsa labaru ta yanar gizo, Lauretta Onochie ta kira mawakin a ranar Talata da ya bayyana manufofinsa ga al’ummar Najeriya a gidan talabijin na kasa dalilin adawarsa da gwamnati.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Fatai Owoseni a ranar Laraba ya ce ba zai ba da damar yin wannan zanga-zanga na nuna adawa da gwamnatin tarayya a Legas ba wada ake shirin yi 5 ga watan Fabrairu saboda ba su sanar da hukumomin tsaro a jihar ba.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel