Yadda Osinbajo ke rike da Kasar yayin da shugaba Buhari ba ya nan

Yadda Osinbajo ke rike da Kasar yayin da shugaba Buhari ba ya nan

– Mukaddashin shugaban kasa yana cigaba da aiki a matsayin shugaban kasan rikon kwarya

– Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi hutun kwana 10

– To ya Farfesa Osinbajo yake ta kokarin fama da takalmin shugaban kasar?

Yadda Osinbajo ke rike da Kasar yayin da Shugaba Buhari ba ya nan

Yadda Osinbajo ke rike da Kasar yayin da Shugaba Buhari ba ya nan

Yemi Osinbajo ne Mukaddashin shugaban kasa a yanzu haka tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi hutun Kasar Birtaniya. Ga wasu gagaruman ayyuka da Mataimakin yayi daga tafiyar Mai gidan na sa kawo yanzu. Dam aba tun yau ya fara rike wannan kujera ba:

• Zauna da Hafsun Sojoji da Gwamnonin Neja-Delta

Mukaddashin shugaban kasa ya zauna da Hafsun Sojin Kasar nan kuma Gwamnonin Neja-Delta can kwanakin baya domin kawo karshen tsageranci a Yankin.

• Taron Majalisar zartarwa na Tarayya

Shugaba Osinbajo ya jagoranci taron Majalisar zartarwa na Tarayya watau FEC a wannan karo da Shugaba Buhari baya nan. Ministocin Kasar da sauran kusoshi sun hallara kamar yadda aka saba

• Taron ‘Yan Kasuwa

Osinbajo ne ya jagoranci taron ‘yan kasuwa karo na biyu da aka yi. Ana nema a hada karfi da karfe tsakanin masu jari da Gwamnati domin gyara tattalin arziki.

• Kasafin kudin bana

Osinbajo ya gana da manyan Majalisa a bayan labule a Fadar Shugaban kasa na Aso Villa. An dai yi wannan taro ne domin kasafin kudin wannan shekarar na bana kamar yadda muka kawo a baya.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel