PDP tana shiryawa 2019 ba da wasa ba

PDP tana shiryawa 2019 ba da wasa ba

– Jam’iyyar PDP na shiryawa zaben 2019 mai zuwa da karfi ba da wasa ba

– PDP na shirin rusa APC a zabe mai zuwa

– Jam’iyyar PDP na kokarin hada kai da sauran Jam’iyyun adawa

PDP tana shiryawa 2019 ba da wasa ba

PDP tana shiryawa 2019 ba da wasa ba

Jam’iyyar PDP mai adawa a Kasar nan na shiryawa zabe mai zuwa na 2019 ga dan-ga dan ba da wasa ba. PDP tana ganin yanzu ne lokacin da ya kamata ta dage domin buge APC daga mulki.

Shugaban Jam’iyyar, Ahmed Makarfi yana kokarin hada kai da sauran kananan Jam’iyyu na Kasar domin hada karfi da karfe. Makarfi wanda shine Shugaban wani bangare na PDP yana ganin haka ne sirrin buge Jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

KU KARANTA: Tsakanin Shehu Sani da Sakataren Gwamnati

Ko da dai PDP ba ta sanar da hakan ba, amma da alamu take-taken na ta kenan. Kwanan nan Jam’iyyar ta gama wani taro domin zage danste da kara kaimi wajen karbe mulkin Kasar a zabe mai zuwa. PDP tace ta gane kuren ta, haka kuma ta san yadda za ta bullowa APC mai mulki.

Wani Dan Majalisar Jihar Legas Honarabul Victor Akande yace akwai babban aiki a wuyan Gwamna Ayo Fayose wanda aka nada Shugaban Gwamnonin PDP na Kasa. Dan Majalisar yayi kira ga Gwamnan ya dawo da Jam’iyyar matsayin ta na da. Ko ya za a kaya? Don kuwa har yanzu PDP na da sauran aiki.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998
NAIJ.com
Mailfire view pixel