Dasuki: Ba inda za ka, Inji Kotu

Dasuki: Ba inda za ka, Inji Kotu

– Kotu ta hana wani da ake zargi fita Kasar waje

– Wanda ake zargi yana son fita waje ne domin zuwa Asibiti

– Babban Kotun Tarayya tace bai isa ba

Dasuki: Ba inda za ka, Inji Kotu

Dasuki: Ba inda za ka, Inji Kotu

Wani Dan kasuwa Olugbenga Obadina da ake zargi da karbar kudi hannun Sambo Dasuki ya nemi Kotu ta ba sa izini ya fita Kasar wajen domin ya leka Asibiti, sai dai Kotun tace fau-fau ba za ayi haka da it aba.

Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da rokon hamshakin Attajirin da ake zargi da laifin safarar kudin sata Inji Jaridar The Nation. Ana zargin Obadina da karbar Naira Biliyan 2 daga Ofishin mai bada shawara kan harkar tsaro a wancan lokaci, Sambo Dasuki ba tare da aikin fari ko na baki ba.

KU KARANTA: Minista da 'Dan sa sun ci Biliyan daya

Wanda ake zargi yayi ikirarin yana da cutar ulsa, sai da Lauyoyin da ke karar sa sun ce ko a Najeriya za a iya maganin wannan cuta. Sai dai Alkali mai shari’a Nnamdu Dimgba yace yana iya la’akari da maganar. Kotu dai ta karbe takardun fitar Kasar mutumin da ake zargi tuni.

Shi kan shi Sambo Dauki yana garkame a hannun Hukuma har yanzu, Lauyoyin Gwamnati suna nema Kotu ta bada dama a kira shaidu a boye saboda girman shari’ar.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana zaune kalau: Wani Dalibi ya aika abokin sa lahira cikin dare

Ana zaune kalau: Wani Dalibi ya aika abokin sa lahira cikin dare

Ana zaune kalau: Wani Dalibi ya aika abokin sa lahira cikin dare
NAIJ.com
Mailfire view pixel