LABARI DA DUMI-DUMI: 'Yan bindiga sun kashe wasu ' yan kasashen waje a Adamawa

LABARI DA DUMI-DUMI: 'Yan bindiga sun kashe wasu ' yan kasashen waje a Adamawa

Wasu 'yan bindiga dadi sun hallaka mutane 5 a jihar Adamawa.

LABARI DA DUMI-DUMI

Rahoto daga jihar Adamawa na nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun hallaka wasu ‘yan kasashen waje 2 wadanda a ke zato da yin kwangila da gwamnatin jihar da kuma wasu jami’ai gwamnati 5.

Jaridar Daily Post ta rahoto cewa, an hallaka wadannan mutane ne a wani kauyen a karamar hukumar Toungo a jihar Adamawa.

Daya daga cikin wadanda aka kashe da aka gano a matsayin Zakaria, babban Darekta a ma’aikatar fili da binciken na jihar Adamawa.

KU KARANTA KUMA: Matashi ya kashe kansa bayan budurwa tace bata son shi

Wannan al’amarin ya faru ne a lokacin da jami'an ke kokarin gindaya iyakar wasu kauyuka tsakanin Kamaru da Nijar.

Har yanzu ba gane wadanda suka kai hari ba, amma jihar Adamawa na daya daga cikin jihohin da ‘yan Boko Haram ke barna bayan jihar Borno da kuma Yobe.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel