Daga yanzu: Sai wadanda suka iya noma za a fara dauka a Jami’i’oi

Daga yanzu: Sai wadanda suka iya noma za a fara dauka a Jami’i’oi

– Daya yanzu dai Gwamnatin tarayya tace sai dalibi na sha’awar gona zai shiga Jami’a

– Wannan doka ta shafi Jami’un koyon harkar gona

– Ministan gona na Kasar Audu Ogbeh ya bayyana haka

Daga yanzu: Sai wadanda suka iya noma za a fara dauka a Jami’i’oi

Daga yanzu: Sai wadanda suka iya noma za a fara dauka a Jami’i’oi

Ministan gona da raya karkara na Kasa Audu Ogbeh yace daga yanzu sai dalibi ya zama yana da sha’awar aikin gona kafin ya samu shiga zuwa Makarantun Jami’ar koyon aikin gona na Kasar.

Ministan ya bayyana haka a wani taro da yayi da Shugabannin Jami’o’in na Tarayya a Jiya Talata. An dai dauki wannan mataki ne domin komawa harkar noma gadan-gadan. Don haka ne ma Ma’aikatar noman ta karbe Jami’o’in noma na Kasar wadanda ke Garin Umahia, da Makurdi da Abeokuta zuwa hannun ta.

KU KARANTA: Osinbajo ya gana da Saraki da Dogara

Ministan ya koka da yadda wadannan Jami’o’i suka koma koyar da kwas-kwas irin na bangaren kimiyya da fasaha maimakon asalin aikin gona. Har wa yau Ministan yayi alkawarin taimakawa wadannan Jami’o’i domin su ji dadin aikin sun a bincike.

Haka kuma mun samu labara cewa Gwamnatin tarayya za ta dabbaga tsarin nan na babu aiki-babu albashi ga Malaman Makaranta masu yajin aikin.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Tun da maganar noma ake yi, ku shakata da wannan Bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel