An koro ‘Yan Najeriya daga Turai

An koro ‘Yan Najeriya daga Turai

– An samu labari cewa an koro ‘Yan Najeriya 83 daga Kasar Birtaniya

– Ciki dai akwai wadanda ke tsare a Gidajen Yari

– An dai fatattako ‘Yan Najeriyan da takardun zaman su gama aiki

An koro ‘Yan Najeriya daga Turai

An koro ‘Yan Najeriya daga Turai

Mun samu labari cewa yanzu haka an fatattako ‘Yan Najeriya guda 83 daga Kasar Birtaniya watau UK. Wadanda aka koro dai takardun zaman na su a Kasashen sun kare ne ko kuma suna tsare a gidan kurkuku.

Za a dai maido Mutanen Najeriyar ne ta filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas a yau dinnan. Mafi yawancin wadanda za a dawo da su din dai takardun zaman su sun kare ne ko kuma wadanda wa’adin zaman su na kurkuku a Kasar Ingilan ya kusa karewa.

KU KARANTA: An tserewa Arewa a Najeriya

Wani Jami’in Hukumar NEMA mai bada agajin gaggawa na Kasa ya bayyanawa Jaridar Punch cewa tun da asuba za a karbi bakin. Daga nan ne dai za a fahimci babban dalilin da ya sa aka koro su daga Kasar UK din.

A Ranar Laraba ta wancan makon ne sabon shugaban Kasar Amurka ya fatattako bakin haure har guda 92. Cikin wanda Shugaba Donald Trump ya koro daga Kasar ta sa akwai mutanen Kasar Somalia, da kuma Kenya.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel