An hallaka mutane 3 a wata rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar Adamawa

An hallaka mutane 3 a wata rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar Adamawa

- Akalla mutane uku suka hallaka a wata sabuwar rikici a Jihar Adamawa.

- An hallaka mutanen 3 a wata rikici tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma mazaunar garin Gereng da ke karamar hukumar Girei.

- Wasu mutane 6 suka ji rauni a cikin rikicin

An hallaka mutane 3

Gwamnan jihar Adamawa Jibrilla Bindow

Jaridar Thisday ta rahoto cewa an hallaka mutanen 3 a wata sabuwar rikici tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma mazaunar garin Gereng da ke karamar hukumar Girei a jihar Adamawa. Kuma akalla mutane 6 suka jikkata.

Wani mashaidi ya ruwaito cewa wasu 'yan Gereng na kama kifi a cikin wani kandami a kusa da kogin Binuwai a ranar Talata, 31 ga watan Janairu a lokacin da wasu makiyaya matafiya suka kai farmaki a kan mutanen.

KU KARANTA KUMA: Matashi ya kashe kansa bayan budurwa tace bata son shi

Mashaidi ya ce mutanen garin sun yi tururuwa suwa fagen gadan, amma makiyayan sun tsere kafin isowarsu.

Majiyar ta ce yayin da a ke zato cewa makiyayan sun fice daga yankin, se kwasam makiyayan sun tattara ‘yan uwansu makiyaya zuwa su yaki mutanen garin Gareng.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a June 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a June 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998
NAIJ.com
Mailfire view pixel