EFCC ta gurfanar da Minista da ɗansa gaban ƙuliya manta sabo

EFCC ta gurfanar da Minista da ɗansa gaban ƙuliya manta sabo

Hukumar yaki da zamba da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon ministan babban birnin tarayya sanata Bala Muhammad tare da ɗansa mai suna Shamsuddeen Bala Muhammad a gaban kuliya manta sabo a yau 1 ga watan Fabrairu a garin Abuja.

EFCC ta gurfanar da Minista da ɗansa gaban ƙuliya manta sabo

EFCC ta gurfanar da Bala da yaronsa Shamsuddeen ne gaban alkali mai shari’a N. Dimgba na babban kotun tarayya dake Abuja kan tuhumarsu da take yi na zambatan gwamnati naira biliyan 1.2.

KU KARANTA: Ya wanka ma jami’in ɗansanda mari bayan ya kartar masa mota

Kakakin EFCC, Wilson Uwuajeren yace Bala Muhammad ya hada kai da wasu kamfanuwa guda hudu Bird Trust Agro Allied Limited, Intertrans Global Logistic Ltd, Diakin Telecommunications Ltd and Bal-Vac Mining Nigeria Ltd wajen aikata aika aikan satar kudaden.

EFCC ta gurfanar da Minista da ɗansa gaban ƙuliya manta sabo

EFCC ta gurfanar da Minista da ɗansa gaban ƙuliya manta sabo

Kakakin yace daya daga cikin tuhume tuhume 15 dake rataye akan wuyar Bala da yaron nasa shine:

“wani lokaci a shekarar 2015 Shamsuddeen Bala, Bird Trust Agro Allied Ltd da Intertrans Global Logistics Ltd sun biya makuden kudade naira miliyan 296 ba tare da saka kudin a banki ba ga wasu kamfanuwan gine gine A & K Constructions Ltd Abuja da Sunrise Estate Development Ltd don gina wani kasaitaccen gida a fili mai lamba 2116 da 2276 a unguwar Asokoro dake Abuja, wanda wadannan makudan kudade sun fi karfin hankali don haka laifin yaci karo da sashi na 1 na kundin hukunta laifukan satar kudade, kuma hukuncinsa ya fado karkashin sashi na 16(2)(b) da (4) na kundin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel