Dalilin da yasa bana ganin laifin shugaba Buhari kan koma bayan tattalin arzikin Najeriya – Fasto Adelaja

Dalilin da yasa bana ganin laifin shugaba Buhari kan koma bayan tattalin arzikin Najeriya – Fasto Adelaja

Shahararren mai wa’azin nan na Najeriya, Fasto Sunday Adejala wanda ya kasance shugaba kuma babban fasto babban cocin Embassy of God a Kiev, Ukraine, yace bazai bi sahun masu ganin laifin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan koma bayan tattalin arziki ba saboda ji yana da tunani kuma cewa yana amfani da kwakwalwar sa.

Dalilin da yasa bana ganin laifin shugaba Buhari kan koma bayan tattalin arzikin Najeriya – Fasto Adelaja

Fasto Adelaja yace baya ganin laifin shugaban kasa Buhari saboda yana amfani da hankalinsa

Yayi al’ajabin dalilin da zaisa ya ga laifin gwamnatin Buhari kan matsalolin Najeriya alhalin mugayen mutane ne suka gurgunta tattalin arzikin.

Adejala yace: “idan har yan adawsa ko wasu mugayen mutane zasu tayar da albarkattun kasar, idan suka tayar da injin din tattalin arzikin kasar, idan suna yanke kaso arba’in 40% na kudin shiga na kasar, ta yay azan goyi bayansu, ta yaya zanga laifin gwamnati a kan haka. Maimakon haka zan ga laifin mugayen mutanen dake aikata hakan.”

Ya ga laifin Avengers, tsofaffin yan bindigan Niger Delta da kuma masu fafutukan Biyafara kan wasu matsalolin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: An kama wasu yan fashi mata guda biyu a Port Harcourt

Fasto din ya yi bayanin cewa mutane dake son gurbata kokarin gwamnati na cika alkawaran da ta dauka ne ke daukar nauyin Avengers saboda tattalin arziki ya karye.

Ya kara da cewa saboda hare-haren da tsagerun Avengers ke kaiwa bututunan mai ne yasa mai da Najeriya ke samarwa ya sauka daga miliyan 2.2 zuwa miliyan 1.1 wanda ya rage kudin shiga na kasar da kaso arba’in 40% hakan ne ya janyo wahalar da ake fuskanta a kasar. Yace wannan ne dalilin da yasa mutane basu ji dadi ba suke kuma zanga-zanga a kan gwamnatin.

Adelaja na al’ajabin dalilin da yasa har yanzu mutane ke ganin laifin Buhari kan koma bayan tattalin arziki kamar shine ya shirya Averngers ya kuma sasu tayar da bututunan mai.

Tsofaffin yan bindigan Niger Delta

Yace sun bar aikin ta’addanci bayan an biyasu sannan kuma suka kwantar da hankalinsu, sannan kuma suka dawo lokacin da shugaban kasa Buhari ya karbi mulki saboda sunce zai daina biyansu. Sannan suka fara tayar da bututunan mai suna rage kudin shiga na kasar.

Masu neman Biyafara

Fasto din yace yaran Biyafara basa da aiki a maimakon haka sai suke karade unguwanni suna korafin cewa ana kashe su.

Da yayi magana kan kshe-kashen Kaduna, yace bai yarda da hakan ba kuma ko Buhari a matsayinsa na shugaban kasa bazai so kasar sa ta tarwatse a lokacin mulkinsa ba.

Adelaja yace karda wannan ya zamo abunda zaisa kiristoci su fara yaki ko kuma su nemi a raba kasar.

A cewar sa, anyi wa Kiristoci shigar sauri sannan kuma ana amfani dasu don kudirin siyasar wasu.

kalli bidiyo a kasa:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel