UNICEF za ta agazawa yara da Dala biliyan 3 a 2017

UNICEF za ta agazawa yara da Dala biliyan 3 a 2017

- Hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta yi alkawarin taimakawa yaran da ke fama da larurar karancin abinci a kasashe 48

- Najeriya na daya daga cikin kasashen da yara za su amfana daga tallafin a sakamakon rikicin Boko Haram da ya rutsa da su

UNICEF za ta agazawa yara da Dala biliyan 3 a 2017

UNICEF za ta agazawa yara da Dala biliyan 3 a 2017

Hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF za ta kashe sama da dala biliyan uku kan kananan yara kimanin miliyan 48 a yankunan da ke fama da rikici a shekarar 2017

Yaran kasashen da za su amfana sun hada na Najeriya, da Siriya, da Yemen, da kuma sauran wasu kasashe da ke fama da tashe-tashen hankula.

A bisa tsarin hukumar bangaren kula da bayar da agajin jin kai ga kananan yara, hukumar ta sa kokon barar tara kudin ne, da aniyar samarwa kananan yara hanyoyin samun tsaftataccen ruwa sha, da abinci mai gina jiki, da ilmi, da lafiya, da kuma tsaro a kasashe 48 na duniya.

Mista Manuel Fontaine daraktan kula da bayar da agajin gaggawa na UNICEF ya ce, yara kanana sun fi shiga hatsari a yayin da ake fada, da kuma sauran abubuwan tashe-tashen hakula da ke tilastawa mutane barin gidajen su.

Kuma hakan yasa su fuskantar tashin hankali, da cututtuka, da kuma cin zarafi baya ga ci da guminsu.

Ya kuma ce, yara kimanin miliyan 7 da 500,000 za su fuskanci matsanancin rashin abinci mai gina jiki a wasu kasashen da ake magana a kai.

Ku ci gaba da bin mu a http://www.facebook.co/naijcomhausa ko kuma http://www.twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel