Wani mutum ya tuɓe tsirara ya ruga aguje, ko lafiya? (Karanta)

Wani mutum ya tuɓe tsirara ya ruga aguje, ko lafiya? (Karanta)

Wani mutum mai matsakaicin shekaru ya ranta ana kare bayan ya tube kayan sa yayi tsirara a cikin garin Abuja, inda ya shafe sama da kilomita 2 kafin nan ya taka ma kansa birki.

Wani mutum ya tuɓe tsirara ya ruga aguje, ko lafiya? (Karanta)

Wani mutum ya tuɓe tsirara ya ruga aguje, ko lafiya? (Karanta)

Lamarin ya faru ne a mahadar titin Chida, dake yankin Utako na babban birnin tarayya da misalin karfe 2 na rana, wanda hakan ya sanya mutane cikin rudani, inda wasu ke ganin kamar asiri ne aka yi ma mutumin.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya bayyana dalilin daya sanya rikicin kudancin Kaduna karewa

Wani shedan gani da ido ya bayyana cewar “mutumin ya fito daga tasi lami lafiya, amma jim kadan kawai sai ya fara cire kayansa, ko dan kamfai bai bari ba, ya ajiye duk wayoyinsa akan kayan, ajiye wayoyin sa keda wuya kai sai ya fita da gudu.”

Majiyar tamu tace basu ga wani alamaun shaye shaye ba a tattare da mutumin, kuma ba alamar hauka a tare da shi, saboda bayan tsaya, ya dawo cikin hayyacinsa, sai ya boye a bayan wata mota saboda jin kunya, inda wasu mutane suka mika masa kayansa.

Sai dai majiyar tace mutumin ya fada musu cewar ba yau ya fara yin wannan halin ba. “bayan ya huta na kusan mintuna 15, sai ya kwashi kayansa yayi tafiyarsa.

Wani shedan gani da ido mai suna Bayo yace basu kai karar mutumin ga yansanda ba, kuma yace mutumi yaki yarda akai shi wajen fasto yayi masa addu’a.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018
NAIJ.com
Mailfire view pixel