Ana bin 'yar Nigeria bashin N315 miliyan

Ana bin 'yar Nigeria bashin N315 miliyan

- Wani asibiti da ke Burtaniya na bin wata mata 'yar Najeriya da ta haihu a jirgin sama bashin $360,000 kwatankwacin naira 315 miliyan.

- Priscilla ta shiga nakuda ne a jirgin wanda ke kan hanyarta ta zuwa Najeriya daga Amurka kuma ta haihu 'yan hudu a jirgin da ya sauka a fillin jiragen sama na Heathrow da ke Ingila.

Ana bin 'yar Nigeria bashin N315 miliyan

Ana bin 'yar Nigeria bashin N315 miliyan

Daga nan ne kuma aka garzaya da ita asibiti a birnin London, inda daya daga cikin jariran nata ya mutu baya ga dayan da ya mutu tun a cikin jirgin.

Kasancewar ba 'yar Birtaniya ba ce, dole ta biya kudin kulawar da ake bata ita da yaranta asibitin.

Yawan kudin da ake binta din ne kuma ya ja hankalin wasu daga ciki jaridun kasar, ko da yake jaridun The Sun da kuma The Daily Mail basu bayyana lokacin da ta haihun ba.

A wani labarin kuma, Gwamnatin hadin gwiwar Austria ta amince ta hana mata saka burka a wurin taruwar jama'a kamar makarantu da kotuna.

Kasar tana kuma duba yiwuwar hana ma'aikatan kasar saka dankwali da wasu tufafi masu alaƙa da addini.

Ana ganin wannan shawara a matsayin wani yunƙurin daƙile 'yancin da jam'iyyar masu ra'ayin rikau, wanda dan takararsu ya sha kaye da kyar a zaben shugaban kasar na watan da ya gabata ke ci gaba da samu.

A makon da ya gabata ne gamayyar jam'iyyu masu matsakaicin ra'ayi suka kusa rugujewa sakamakon wani rikici a kan wata yarjejeniya game da makomar gwamnatin.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998
NAIJ.com
Mailfire view pixel