Ya wanka ma jami’in ɗansanda mari bayan ya kartar masa mota

Ya wanka ma jami’in ɗansanda mari bayan ya kartar masa mota

Yan Najeriya da dama musamman masu biye da kafafen sadarwa na zamani sun shiga cikin rudani yayin da wani hamshakin attajiri ya wanka ma wani dansanda mari bayan ya kartar masa motarsa ta alfarma.

Ya wanka ma jami’in ɗansanda mari bayan ya kartar masa mota

Ya wanka ma jami’in ɗansanda mari bayan ya kartar masa mota

Wannan lamari mai daurin kai ya faru ne a ranar Litinin 30 ga watan Janairu, inda bidiyon marin ya watsu sosai a yanar gizo, kawia don jami’in dansandan ya bugan mai mota da hannu.

KU KARANTA: Sifeto janar na kasa ya nada CSP Moshood sabon Kaakakin hukumar

Wani shedan gani da ido ne ya dauki bidiyon a daidai lokacin da motocin guda biyu kirar ‘Lamborghini’ suka wuce ta gabansa a unguwar Victoria Island nan kusa da Lekki a ranar Litinin, can kawai sai ya hangi wani dansanda mai karambani ya karci daya daga cikin motocin.

Nan da nan direban motar Lamborghinin ya sauko daga motar ba tare da wani bata lokaci ba ya wanka ma dansandan mari guda biyu kyawawa, sa’annan ya koma cikin motarsa yayi tafiyarsa.

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya wakana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998
NAIJ.com
Mailfire view pixel