Gwamna El-Rufai ya bayyana dalilin daya sanya rikicin kudancin Kaduna karewa

Gwamna El-Rufai ya bayyana dalilin daya sanya rikicin kudancin Kaduna karewa

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya bayyana cewar rashin hukunta masu hannu a cikin rikicin Kaduna shine dalilin daya sanya aka kwashe sama da shekaru 35 ba’a warware matsalar rikicin ba.

Gwamna El-Rufai ya bayyana dalilin daya sanya rikicin kudancin Kaduna karewa

Gwamna El-Rufai yayin karbar bakoncin sanatocin

Gwamna El-Rufai ya bayyana haka ne a ranar Talata 31 ga watan Janairu lokacin da kwamitin binciken rikicin kudancin Kaduna na daga majalisar dattawa suka kawo mai ziyara a karkashin jagorancin Sanata Kabiru Gaya, inji wani rahoton jaridar New Telegraph.

El-Rufai ya gargadi masu tada zauni tsaye a jihar dasu shiga taitayinsu, idan ba haka ba kuma zai sanya wando daya dasu.

KU KARANTA: Babban mashawarcin Sanata Bukola Saraki ya ajiye aiki, ko lafiya? (Karanta)

A cewar jaridar The Nation, gwamna El-Rufai ya musanta zargin da ake yi masa na nuna son kai, inda yace shi baya nuna bambamcin addini ko na kabilanci, balle ma ya hada kai da wasu don a kashe wasu. Gwamnan ya bayyana ma yan majalisun cewar gwamnatinsa ta gaji manyan matsalolin tsaro guda uku; satar dabbobi, sara suka da kuma rikicin kabilanci.

“Lokacin da na hau karagar mulki na tarar da gagaruman matsalolin tsaro guda uku da suka hada da satar dabbobi, sara suka da kuma rikicin kabilanci. Don haka a matsayina na babban jami’in tsaron jihata, amma bani da hurumin juya akalar hukumomin tsaro kamar su soja da yansanda.

“Don haka sai muka ware kudade kuma muka kashe wajen siyan ma jami’an tsaro rigar saka, da motocin zirga zirga. Zuwa yanzu mun kashe sama da N4bn a tallafin da muka baiwa jami’an tsaron mu. Jihar Kaduna zata cigaba da taimaka ma hukumomin tsaro, duk da cewar wannan aikin gwamnatin tarayya ne.” Inji El-Rufai

Gwamnan yayi kira ga gwamnatin Najeriya data kara yawan kudaden da take kashe ma fannin tsaron kasar nan don su samu kwarin gwiwar fuskantar matsalar tsaron data dabaibaye kudancin Kaduna, dama sauran matsaloli tsaro a kasa gaba daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel