Matashi ya kashe kansa bayan budurwa tace bata son shi

Matashi ya kashe kansa bayan budurwa tace bata son shi

Wani matashi dan kasar Zimbabwe, Pious Sibanda, ya hallaka kansa bayan budurwarshi yak i amincewa da auren sa.

Matashi ya rataye kansa bayan budurwa tace bata son shi

Matashi ya rataye kansa bayan budurwa tace bata son shi

Pious Sibanda,ya kashe kansa ne bayan budurwarshi, Immaculate Ncube, tace masa itafa ba zata iya aurensa ba.

Game da cewar jaridar NewsDzeZimbabwe, matashin ya buga mata karfe a ki har ta sume ,daga baya kuma yaje ya rataye kansa tunanin cewa ya kashe ta.

Wanda abu ya faru ne a ranan Juma’a,24 ga watan Junairu. Daga baya aka tsinci gawarsa a kan wata bishia a rataye.

KU KARANTA: Wani dan sanda yayi ma mata jina-jina

Ncube tace SIbanda ya fusata bayan ta fada masa ya je ya gana da iyayenta idan da gaske yana son aurenta. Tace: “ Pious ya fada mini cewa a watan nan zai aure ni kuma na fada masa cewa ya je ya gana da iyayena a Lupane. Ya ki bin hanyar da ya kamata inda ya nace cewan sai dai in fara zama a gidanshi ba tare da sanin iyayena ba.

“Sai nace masa na fasa aurensa kuma na neme say a bani lokaci inyi tunani akan al’amarin. Wannan abu ya fusata shi kuma tun lokacin ya fara fushi dani har dukana yanayi.”

“Ana mako daya kafin ya doke ni, Pious yayi mini barazanar cewa idan ban shiga gidanshi ba, sai ya kashe ni kuma ya kashe kansa. Sai na biye masa saboda tsoro. Amma daga baya sai na fita na koma wajen aiki na. Pious ya zo wajen aikina da inda nike rike da yarinyta, ya umurce ni in bisa zuwa gidansa sai na ki.”

Immaculate tace da karfi da yaji ya kaita bakin kofa inda ya fara buga mat karfe a kai har ta sume a kasa.

“Jini na ta zuba a kaina kuma ko iya gani baniyi amma na samu na karasa wajen makwabta na kuma suka kai ni asibitin Madlambuzi Clinic…… daga baya na samu labarin cewa Pious ya rataye kansa.”

An tsinci gawar Sibanda ne rataye kan wai bishiya.

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel