Yarinya 'yar shekara 9 ta tayar da bam a sansanin yan gudun hijira

Yarinya 'yar shekara 9 ta tayar da bam a sansanin yan gudun hijira

- Wata ƙaramar yarinya da ake jin 'yar shekara 10 ce kacal a duniya ta tarwatsa kanta a arewa maso gabashin Nijeriya

- Shaidu sun ce yarinyar ta tunkari wani sansanin 'yan gudun hijira ne da ke garin Banki a jihar Borno, lokacin da sojoji suka tare ta

Yarinya 'yar shekara 9 ta tayar da bam a sansanin yan gudun hijira

Yarinya 'yar shekara 9 ta tayar da bam a sansanin yan gudun hijira

Sojojin sun nemi ta ɗaga hijabinta sama, inda suka ga abubuwan fashewa da ta ɗaura a ƙugunta. Daga nan sai ta ja kunamar, bam ɗin ya tashi.

Aƙalla mutum ɗaya ya mutu a wani harin ƙunar-baƙin-wake daban da aka kai a cikin birnin Maiduguri.

Ƙungiyar Boko Haram tana amfani da ƙananan yara da matasa, inda take sanya su kai harin ƙunar-baƙin-wake a masallatai da kasuwanni.

A baya-bayan nan ma sai da shalkwatar tsaron Nijeriya ta yi gargaɗi kan yadda ake amfani da mata ɗauke da goyon jarirai wajen kai harin ƙunar-baƙin-wake a arewa maso gabas.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

NAIJ.com
Mailfire view pixel