Wani dan sanda yayi ma wata mata jina-jina

Wani dan sanda yayi ma wata mata jina-jina

Budurwa yar shekara 30 mai suna Oluchukwu Ezemaduka,wacce ke jinya a asibiti bayan wani dan sanda mai suna Idiahgbe Iyobosa yayi gotar mata da haba.

Tirkashi : Wani dan sanda yayi wata mata jina-jina

Tirkashi : Wani dan sanda yayi wata mata jina-jina

Idiahgbe Iyobosa,wanda dan sanda ne a banki a FESTAC Town, yayiwa matan dukan raba ni da yaro ne yayinda jinni ya fara zuba a bakinta. A yanzu dai tana asibitin West Care Specialist Hospital, Akowonjo, Egbeda Legas.

KU KARANTA: An damke masu daukan nauyin Boko Haram a Borno

Jaridar Punch ta bada rahoton cewaa Iyobosa, a ranan asabar 21 ga watan Junairu ya je kaiwa budurwarshi ziyara mai suna Maryjane Anyagwa, wacce ke da zama a Ejigbo. Amma da ya isa gidan, sai ya tarar da Ezemaduka kadai a gidan.

Da yayi tambaya inda taje, sai Ezemaduka tace masa bata san inda taje ba,kawai sai ya fusata.

Tace: “ Bani a daki lokacin da yazo. Yayinda nazo shig dakin, sai na lura cewa mutum ya shiga,sai na amsi fitila daga hannun makwabta na haska kawai sai gas hi cikin dakin. Yayi kacakaca da ko ina . ya tanbayeni inda budurwarshi take ni kuma naki amsa mana. Da ya kara tambayana sai nace ban san inda take ba.

Kawai sai ya fara tokarina da takalminsa,ya gotar mini da haba. Sai ya fito da adda ya bioyni waje. Mutane ne suka cece ni. Wannan azaba yayi yawa. Likita yace za’ayi mini tiyata a wannan mako."

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a June 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a June 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998
NAIJ.com
Mailfire view pixel