Majalisar dokoki ta amince shugaba Buhari ya amshi bashin $1 billion

Majalisar dokoki ta amince shugaba Buhari ya amshi bashin $1 billion

- Fadar shugaban kasa da majalisan dokoki sunyi yarjejeniya

- Wannan yarjejeniya zai baiwa fadar shugaban kasan daman amsan bashin $1 billion domin farfado da tattalin arzikin kasa

- Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wasikar bukatar neman bashing a majalisar a ranan Alhamis,26 ga watan Junairu

Majalisar dokoki ta amince shugaba Buhari ya amshi bashin $1 billion

Majalisar dokoki ta amince shugaba Buhari ya amshi bashin $1 billion

Wata rahoton jaridar Dailypost na nuna cewa fadar shugaban kasa tare da majalisar dokokin Najeriya ta yi wata sabuwar yarjejeniya wanda zai baiwa shugaba Buhari daman amsan bashin kudin $1 billion domin gudanar da ayyukan na farfado da tattalin arzikin tarayya.

Game da rahoton, Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wasikar bukatar neman bashing a majalisar a ranan Alhamis,26 ga watan Junairu.

Yarjejeniyar ta yiwu ne bayan ganawar da mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yayi da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki , da kakakin majalisan wakilan, Yakubu Dogara.

Majiyar tace: “ Wasikar tazo ne bayan mun gama taron majalisa da kuma ganawa tsakanin shugaban majalisan dattwa, kakakin majalisa da kuma mukaddashin shugaban kasa, sun gana ne domin tattaunawa akan yadda za’a amince da bukatan shugaban kasan."

Yace shugaba Buhari ya amince da da bashin tari din en bayan majalisar dokokin tayi watsi da bashin $29.9 billion da Buhari ya bukata a farkon shekara.

“Saboda maganganun mutane da kuma watsin da majalisa tayi, bangaren zantarwa ta fasa amsan bashin $29.9 Billion.”

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel