An hana mata fita waje da 'niqabi' a wannan kasar

An hana mata fita waje da 'niqabi' a wannan kasar

- Gwamnatin hadin gwiwar Austria ta amince ta hana mata saka burka a wurin taruwar jama'a kamar makarantu da kotuna

- Kasar tana kuma duba yiwuwar hana ma'aikatan kasar saka dankwali da wasu tufafi masu alaƙa da addini

An hana mata fita waje da 'niqabi' a wannan kasar

An hana mata fita waje da 'niqabi' a wannan kasar

Ana ganin wannan shawara a matsayin wani yunƙurin daƙile 'yancin da jam'iyyar masu ra'ayin rikau, wanda dan takararsu ya sha kaye da kyar a zaben shugaban kasar na watan da ya gabata ke ci gaba da samu.

A makon da ya gabata ne gamayyar jam'iyyu masu matsakaicin ra'ayi suka kusa rugujewa sakamakon wani rikici a kan wata yarjejeniya game da makomar gwamnatin.

A wani labarin kuma, Shugabanni Al’ummar Musulmin Amurka sun shigar da karar shugaban kasar Donald Trump a gaban kotu saboda abin da suka kira dokar da za ta hana mabiya addinin Islama shiga cikin kasar.

Nihad Awad, daraktan kungiyar Musulmin na daga cikin mutane 26 da suka shigar da karar, wadda suke cewa tana kalubalantar dokar da za ta hana Musulmi zuwa Amurka.

Awad ya ce, wannan matakin ba zai tabbatar da tsaro a dukkanin Amurka ba, face jefa fargaba a zukatan al'umma.

Lauyoyin Amurka sun ce, matakin na Trump ya saba wa sashen kundin tsarin mulkin kasar da ya bukaci kare tare da bai wa jama'a damar gudanar da addininsu.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel