Barcelona ya sayi dan wasan Enyimba, Ezekeil Bassey

Barcelona ya sayi dan wasan Enyimba, Ezekeil Bassey

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da kammala cinikin siyan dan wani dan kwallon Najeriya mai suna Ezekeil Bassey daga kungiyar kwallon kafa ta Eyimba, akan yarjejeniyar aro.

Barcelona ya sayi dan wasan Enyimba, Ezekeil Bassey

Barcelona ya sayi dan wasan Enyimba, Ezekeil Bassey

Ana sa ran Bassey zai yi wasa ne Da yan wasan kungiyar Barcelona na rukunin B, amma zai dinga yin atisaye da manyan yan wasan akai akai, ta yadda idan ya nuna bajinta, zai samu shiga cikin manyan yan wasan Barcelona.

KU KARANTA: 'Da haihuwar yuyuyu, gara da daya kwakkwara’ – Inji Sarki Sunusi

Barcelona ta sanar da siyan Ezekeil Bassey kamar haka: “Kungiyar FC Barcelona da Enyimba sun kammala yarjejeniyar daukan aron Ezekeil Bassey zuwa Barcelona, inda zai yi wasa a cikin yan wasan rkuni na biyu zuwa karshen kakar wasa.

“Yarjejeniyar ta hada da siyan Ezekeil na tsawon shekaru biyu, idan ya nuna bajinta. Nan da awanni kalilan za’ayi ma Ezekeil gwajin lafiya.”

Shi dai dan wasa Bassey kwararren dan wasan gaba ne, kuma yayi fice a tsakanin yan wasan dake buga wasa a gasar Firimiya na Najeriya, kuma yana daya daga cikin wadanda suka buga wasa da kungiyar kasar Sifen.

Zuwa yanzu dai ba’a hangi keyar Bassey ba a gasar firimiya na kasa, saboda yana shirin wucewa Barcelona. Idan Bassey ya samu nasara, zai zamto dan Najeriya na Uku daya buga wasa akungiyar Barcelona.

A baya ma yan Najeriya biyu da ska hada da Emmanuel Amuneke da Gbenga Okunowo sun buga wasa a kungiyar ta Barcelona.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018
NAIJ.com
Mailfire view pixel