An damke masu daukan nauyin Boko Haram a jihar Borno

An damke masu daukan nauyin Boko Haram a jihar Borno

- Rundunar sojin Najeriya sun damke wasu yan siyasa da malamai masu alaka da kungiyar Boko Haram

- Majiyoyi sun bayyana cewa za’a kama wasu mutane a kwanaki masu zuwa

- Kwamandan tiyatan Operation Lafiya Dole, Maj. Janar. Lucky Irabor, ya tabbatar da wannan labara amma yace ba za’a bayyana sunayensu da hotunansu saboda dalilai na tsaro

An damke masu daukan nauyin Boko Haram a jihar Borno

An damke masu daukan nauyin Boko Haram a jihar Borno

An damke wasu yan siyasa guda biyu da wani sarkin gargajiya a wata farmaki bisa ga alakansu da kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa yan siyasan wadanda sanannu ne a gwamnati,sun shiga hannu ne a farkon wannan makon a wata farmakin da Operation Lafiya Dole ta kai.

KU KARANTA: Gobara a kasuwan Yola

Majiyar ta bayyana cewa daya daga cikin wadanda aka kama wanda shima malamin addini ne,ya arce daga garin loacin da ya samu labarin cewa soji ne neman shi.

Amma, an kamashi a hanyar Maiduguri-Jos yayinda yake kokarin guduwa wata jiha.

Shi kuma dayan wani sanannan dan baranda ne mai suna ECOMOG a jihar Born ,kuma hadimin wasu yan siyasa ne, game da cewar majiyar soji.

Kana kuma wani soja ya bayyana cewa an damke wani sarkin gargajiya da wasu malaman addini guda biyu bisa ga labarin liken asirin da aka samu na alakarsu da Boko Haram.

“Ku saurari Karin bayanai yayinda zamu damke wasu da damam a kwanakin nan,” Majiyan tace.

A bangare guda, gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ta samu wasu takardu masu muhimmanci daga Boko Haram ,saboda haka, masu kafafen yada labarai su bi a hankali.

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel