Anyi Gobara a kasuwan Yola

Anyi Gobara a kasuwan Yola

Daya daga cikin manyan kasuwannin garin Yola, jihar Adamawa, wacce akafi sani da “tsohuwar kasuwa” ta ci bal-bal, jaridar Premium Times ta bada rahoto.

Sabuwa : Gobara a kasuwan Yola

Sabuwa : Gobara a kasuwan Yola

Game da cewar idon shaida, wutan ta fara ci ne karfe 7 na yamma bayan mutane sun gama siye da siyarwa sun koma gida, kuma an kulle kasuwa.

Jami’an hukumar kashe wutan gobara sun sauka a wurin domin kashe wuta.

KU KARANTA: A haramta achaba a fadin Najeriya - FRSC

Wasu mutane su nemi a bari sun shiga kasuwan domin fidda kayansu amma an hana kowa shiga.

Wani jami’in tsaro a kasuwan yace: “Yawancinsu na son shiga ne saboda yin sata. Tunda hukumar kashe wuta na wurin kuma da alamun cewa sun ci karfin wutan.”

Kasuwan na kusa da kurkukun garin da kuma masallacin Jimeta.

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel