Zanga-Zanga: Haushi suke ji Jonathan ba ya kan mulki-Femi Adesina

Zanga-Zanga: Haushi suke ji Jonathan ba ya kan mulki-Femi Adesina

– Wasu ‘Yan Najeriya za su yi zanga-zanga domin yadda abubuwa suka tabarbare

– Mai magana a madadin Shugaban kasa yace masu wannan shiri suna jin haushi ne kurum Jonathan ba ya kan mulki

– Femi Adesina yace ba a taruwa a zama daya

Zanga-Zanga: Haushi suke ji Jonathan ba ya kan mulki-Femi Adesina

Zanga-Zanga: Haushi suke ji Jonathan ba ya kan mulki-Femi Adesina

Fadar Shugaban kasar ta maida martani ga masu shirin fita zanga-zangar da za ayi Ranar Lahadi. Shararren Mawakin nan 2 Face Idibia zai jagoranci wannan zanga-zanga domin nuna rashin jin dadi game da yadda abubuwa suka sukurkuce.

Sai dai mai magana da bakin Shugaban kasa, Femi Adesina yace wadanda suka shirya wannan gangami mutane da suka goyi bayan tsohon Shugaba Jonathan a zaben da aka yi, don haka suke jin haushi don ya sha kasa hannun Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Soja ya kusa hallaka wata Budurwa

Femi Adesina dai yake cewa yarbawa sun ce mutane biyu ba su kwanciya barci ta barayin hannu daya don kuwa inda kake numfashi nan wani zai saki iska. Adesina yace adawa ce kawai za ta wasu yin wannan zanga-zangar.

Wasu na zargin wadanda suka shirya zanga-zangar da zama cikin ‘Yan PDP ko kuma yin shiru lokacin da abubuwa suka tabarbare a baya. Akwai wanda ake zargi Gwamnoni da Sanatocin PDP sun basa kyaututtuka a wancan mulkin.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel