Kwastam na neman Ma’aikatan da suka bari aka shigo da Bindigogi

Kwastam na neman Ma’aikatan da suka bari aka shigo da Bindigogi

– Hukumar Kwastam na neman wasu Ma’aikatan ta ruwa-a-jallo

– Wadannan Jami’ai biyu suna da hannu wajen shigo da wasu tarin makamai

– Duk wanda ya ga wadannan Jami’ai ana bukatar ya nemi Hukuma

Kwastam na neman Ma’aikatan da suka bari aka shigo da Bindigogi

Kwastam na neman Ma’aikatan da suka bari aka shigo da Bindigogi

Hukumar Kwastam ta sanar da cewa tana neman wasu Ma’aikatan ta guda biyu ruwa-ajallo. Wadannan Ma’aikata suna da hannu wajen shigo da wasu tarin makamai cikin Kasar ta hanyar Legas.

Idan ba a manta ba Ranar Lahadi ne Hamid Ali wanda shine Shugaban Hukumar ta Kwastam din ya bayyana cewa an samu datse wasu kwalaye dauki da tulin bindigogi. An dai samu sababbin bindigogi har guda 661 fil a cikin kwali ana neman a shigo da su cikin Kasar.

KU KARANTA: Kudu ta tserewa Arewacin Najeriya

Kwastam na neman Ma’aikatan da suka bari aka shigo da Bindigogi

Kwastam na neman Ma’aikatan da suka bari aka shigo da Bindigogi

Yanzu haka dai Hukumar Kwastam na neman Ma’aikatan na ta biyu da ke da hannu wajen shigowa da wadannan makamai; Abdullahi I da kuma Odiba Haruna Inah. Ana neman duk wanda ya gan su ya hanzarta ya sanar da Hukumar Kwastam.

Tuni dama dai aka kama mutane 3 da ke da hannu wajen shigo da makaman daga ciki akwai wanda ya shigo da su cikin Kasar Oscan Okafor da kuma wasu; Mahmud Hassan da Sadique Mustafa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ya ku ke gani? A mikawa Sojoji wadannan Bindigogi kawai ko?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel