Shugaban Kasa yayi waya daga Landan

Shugaban Kasa yayi waya daga Landan

– Shugaba Buhari ya kira Gida Najeriya daga Birnin Landan inda yake hutawa

– Buhari yayi ta’aziya ne ga Ministan wasanni na Kasar Solomon Dalung

– Dalung dai ya rasa matar sa kwanan nan

Shugaban Kasa yayi waya daga Landan

Shugaban Kasa yayi waya daga Landan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira gida Najeriya ta wayar tarho daga Birnin Landan. Shugaba Buhari yayi waya ne da Ministan wasanni da cigaban matasa na Kasar Solomon Dalung inda yayi masa ta’aziya.

Kamar dai yadda aka samu labari, Ministan ya rasa Mai Dakin sa kwanan nan. Shugaba Buhari yayi masa addu’a a game da wannan babban rashi da yayi. Ana dai sana da cewa Shugaba Muhammadu Buhari yana Birnin Landan inda yake hutawa.

KU KARANTA: Za ayi wa Gwamnatin Buhari zanga-zanga

Shugaban Kasa yayi waya daga Landan

Shugaban Kasa yayi waya daga Landan

Mai magana da bakin Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Laolu Akande ne dai ya bayyana haka. Farfesa Osinbajo dai da kan sa yayi wa Minista Dalung ta’aziyar wannan rashi, yana mai yabon Marigayiyar da kuma alkawarin sa ta addu’a.

Cikin kwanakin nan ne, wani mutumi mai suna Usman Bukar ya yankawa wani Direban mota mari har sai da ya kusa mutuwa don kuwa yace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mutu a Landan.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel