Kasafin kudi: Osinbajo ya gana da Shugabannin Majalisa

Kasafin kudi: Osinbajo ya gana da Shugabannin Majalisa

– Mukaddasun Shugaban kasa ya gana da Shugaban majalisar dattawa da kuma Shugaban majalisar wakilai

– Osinbajo ya zauna da su Saraki da Dogara ne game da batun kasafin kudin bana

– An yi wannan taro ne a cikin Aso Villa a bayan labule tare da wasu Ministoci

Kasafin kudi: Osinbajo ya gana da Shugabannin Majalisa

Kasafin kudi: Osinbajo ya gana da Shugabannin Majalisa

Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya gana da manyan Majalisa a bayan labule a Fadar Shugaban kasa na Aso Villa. An dai yi wannan taro ne domin kasafin kudin wannan shekarar na bana.

Rahotanni daga Jaridar Daily Trust suka bayyana cewa Osinbajo ya gana da Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kuma Shugaban majalisar wakilai na Kasar Yakubu Dogara. Ministan Kudi na Kasar Kemi Adeosun da kuma Udo Udoma wanda shine Ministan kasafi yana cikin wadanda suka halarci taron.

KU KARANTA: Manyan Kanun Labarai a Yau

Kasafin kudi: Osinbajo ya gana da Shugabannin Majalisa

Kasafin kudi: Osinbajo ya gana da Shugabannin Majalisa

Bayan taron dai Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya bayyana abin da suka tattauna. Saraki yace sun yi magana ne game da abin da ya shafi tattalin arziki da inda wannan Gwamnati ta dosa.

Kwanan nan Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Dr. Abubakar Bukola Saraki yace shi fa ba abin da ke gaban sa irin ya ga tattalin arzikin Najeriya yayi kyau. Bukola Saraki ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da tashar Channels TV.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a June 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a June 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998
NAIJ.com
Mailfire view pixel