Shin Donald Trump zai sha kuwa?

Shin Donald Trump zai sha kuwa?

– Sabon Shugaban Kasar Amurka zai fuskanci kalubale game da sababbin tsare-tsaren sa

– Tuni Kasashen Duniya sun fara nuna Trump da karamin yatsa

– Ko za a kwashe da Trump lafiya kuwa?

Idan ana bin labarai dai an san cewa a Ranar Juma’ar da ta gabata ne, Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya nemi a hana baki da ‘yan gudun hijira shigowa cikin Kasar Amurka. Trump ya nemi ya hana Kasashe 7 na Musulmai shiga cikin Kasar.

Sai dai Jama’a da dama sun soki wannan tsari, suna ganin ba zai yi wani tasirin kirki ba, wasu ma suna ganin cewa akwai munafunci a tsarin na Trump. Mutanen Amurka sun ta buga zanga-zanga, daga baya kuma aka samu wata Kotu ta bada umarnin dakatar da tsarin na Trump. Bugu da kari ma dai Shugaba Trump din ya kori Shugaban Lauyoyin Kasar bayan ta ki kare tsarin na sa.

KU KARANTA: Obama ya caccaki Trump

A Jiya ma dai Tsohon Shugaban Kasar, Barrack Obama yace sam bai yarda da wannan tsari na Trump ba, ko ta kusa ko ta nesa. Kwanan nan ne dai wani Tsohon Dan wasa Mo Farah ya soki Shugaban Kasar da wannan manufar.

A baya dai Sanatoci da ‘Yan Majalisun Kasar na Jam’iyyar Democrats sun nemi zama domin nuna adawar su da wannan doka. Dama wasu dai na ganin cewa daga karshe dai tsige Donald Trump din za ayi tun kafin ya je ko ina.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel