Mulkin Buhari: Kura ta kai bango; Za a fara zanga-zanga

Mulkin Buhari: Kura ta kai bango; Za a fara zanga-zanga

– ‘Yan Najeriya za su yi zanga-zanga domin nuna rashin yardar su da Gwamnatin Buhari

– Jama’a sun ce ba su gane inda wannan Gwamnati ta dosa ba

– Wasu kuma za su yi zanga-zangar goyon bayan Shugaban

Mulkin Buhari: Kura ta kai bango; Za a fara zanga-zanga

Mulkin Buhari: Kura ta kai bango; Za a fara zanga-zanga

Da alamu dai kura ta kai bango kenan. Shararren Mawakin nan 2 Face Idibia zai jagoranci wani zanga-zanga da za ayi domin nuna rashin goyon bayan Gwamnatin shugaba Buhari. Za dai ayi wannan zanga-zanga ne a farkon wata mai zuwa.

Sai dai kuma a Ranar da za ayi zanga-zangar, an samu wasu da za su yi na su zanga-zangar domin nuna goyon bayan Shugaban kasar. Za dai ayi wadannan zanga-zangar ne a Ranar Lahadi 5 ga Watan Fubrairu.

KU KARANTA: Yan Majalisa na nema a kara kudin mai

Yanzu aka ana samun rade-radin cewa wani Tsohon Gwamnan Jihar Akwa-Ibom ne ya shirya wannan zanga-zangar a bayan fage domin nuna rashin amincewa da Gwamnatin Shugaba Buhari. A lokacin da Mawaki 2 Face yayi aure dai, Godswill Akpabio ya ba sa kyautar katuwar mota, don haka wasu su ke ganin shi ne ya shirya wannan zanga-zanga.

A jiya ne kuma Gwamnan Jihar Imo, Rochas O. Okorocha ya bayyana cewa Inyamurai su iya karbin mulkin Kasar nan idan har Baba Buhari ya gama wa’adin sa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Shugaba Buhari wani lokaci da ya ke magana da mutanen Bauchi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel