'Da haihuwar yuyuyu, gara da daya kwakkwara’ – Inji Sarki Sunusi

'Da haihuwar yuyuyu, gara da daya kwakkwara’ – Inji Sarki Sunusi

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi II ya ja kunnen al’ummar Arewa dasu canza halinsu dangane da yawan aurace aurace da yawan haihuwa, inda ya kiraye su dasu auri daidai matayen da zasu iya rikewa, sa’annan su haifi iya yaran da zasu iya tarbiyyantarwa.

‘da haihuwar yuyuyu, gara da daya kwakkwara’ – inji Sarki Sunusi

Sarki Sunusi ya bayyana haka ne a yayin gudanar da bikin cika shekaru 60 tare da kaddamar da mujallan makarantar sakandari ta Capital School dake Kaduna, inda yace yin hakan ne zai samar da ingantacciyar al’umma a yankin Arewa gaba daya.

KU KARANTA: Sifeto janar na kasa ya nada CSP Moshood sabon Kaakakin hukumar

Sarkin yace bashi da matsala da duk yawan matan da mutum ya aura indai zai iya daukan nauyinsu.

Yace: “Kowa nada daman ya auri mata biyu, sa’annan kana da daman haihuwar yara 100, amma fa ka tabbata zaka iya daukan nauyinsu tare da ilimantar dasu. Idan kuma ka tabbata baka da halin yin hakan, toh mutum ya auri iya abinda zai iya rikewa, sa’annan ya haifi iya yayan da zai iya kulawa da tarbiyyarsu.”

Mai martaba Sarki yace yaya nagari ne kadai al’umma zata yi alfahari dasu, sa’annan idan muka lura da ire iren yaran nan, zamu gane cewar sun samu kulawa, da tarbiya kwakkwara daga iyayensu, kuma suna da shakuwa da alaka mai kyau tsakaninsu da iyayensu.

“Ga shin an muna ta haifan yara kacakaca sai kaje wasu haja, zaka gansu akan titi suna ta bilayi, suna mutuwa babu wanda ya damu, suna shaye shaye babu wanda ya damu.” Inji shi.

Daga bisani Sarki Sunusi yayi kira da babban murya dasu yi duba da idon basira dangane da matsalolin da suka janyo tabarbarewa yankin Arewa, kamar su auren dole, aure da wuri, auren mata dayawa, mutuwar aure, hakkin iyaye akan yayansu. Saboda a cewar Sarkin “jama’an mu a yankin Arewa suna ganin namiji ne keda ikon haihuwa, amma basa ba tarbiyya muhimmanci.”

Daga karshe yayi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyin sa kai dasu fitar da wani tsarin yin hadin gwiwa da malaman addinai wajen samar da ingantaccen ilimi ta hanyar gina makarantu, horar da malamai, daukan nauyin dalibai da dai sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel