‘Yan Najeriya sun maida martani

‘Yan Najeriya sun maida martani

'Yan Najeriya da yawa sun mayar da martani akan wata barazanar wani matashi cewa za a yi yaki idan shugaban Buhari ya mutu a shafinsa ta fesbuk.

‘Yan Najeriya

Haruna Maitala

Mutane da yawa 'yan Nijeriya sun tofa albarkacin bakin su ga wata furofaganda da wani matashi Haruna Maitala ya rubuta a shfinsa ta Fesbuk. Suna mai cewa babu shaka ba su yi fatar mutuwar shugaba Muhammadu Buhari ba, amma idan aka din ta faru, ba za ta zama abin yaki sakanin ‘yan Najeriya ba.

Haruna Maitala ya rubuta a kwanan nan cewa: “A cewa shugaba Buhari na cikin isashen lafiya da kuma jin dadin a Birtaniya, Allah de ya kiyaye, idan Buhari ya mutu Kiristoci da ‘yan kudancin kasar su sani cewa Osinbajo ko wani Kirista ba zai yi mulki ba saboda mulkin nan na ‘yan arewa ne. Ba zamu taba yarda a maimaita abinda ya faru a shekara 2010 ba. ”

“Idan mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya ki ya yi murabus, tooh, ‘yan Najeraya su shira wa wata yakin basasa. Ko kuma Buratai ya yi juyin mulki. Ko a ranshar da wani daga arewa kuma Hausa Fulani, abin da muke so shine ya zama dan uwarmu ne a mulki. Wannan ya zama maku gargadi.”

KU KARANTA KUMA: Za mu ta da yakin basasa idan Shugaba Buhari ya mutu

Mayar da martani ga maganar Maitala, Bilyamini Muazu ya ce: "Ba za a yi wata yaki ba idan shugaba Buhari ya mutu, domin babu wanda zai iya hana shi mutuwa ko canja lokacin mutuwar har in kwanansa ta kare. Allah (SWT) ne kawai ya san rana da kuma lokacin da kowa zai mutu.''

Adebayo Olagbami a nasa bangaren ya ce: "Babu wani abu da zai faru idan wani shugaba ya mutu. A baya tsohon shugaban kasa Janar Abacha ya mutu, Najeriya ba ta rabu ba, tsohon shugaban kasar Yar 'Adua ma ya mutu a karagar mulki, ba abin da ya faru. Ka dena furofaganda cewa sa a yi yaki idan shugaba Buhari ya mutu, ba abin da zai faru. Najeriya nan na mu gaba daya.''

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel