Tashin hankali : Majalisan wakilai ta bada shawara a kara kudin man fetur da N5

Tashin hankali : Majalisan wakilai ta bada shawara a kara kudin man fetur da N5

Da alamun cewa za’a kara kudin man fetur daga N145 zuwa N150 ga lita idan majalisar wakilan tarayya ta zantar da dokan harajin kan titi.

Tashin hankali : Majalisan wakilai ta bada shawara a kara kudin man fetur da N5

Tashin hankali : Majalisan wakilai ta bada shawara a kara kudin man fetur da N5

Kwamitin majalisar wakilan tarayya akan ayyuka ta bada shawaran cewa a kara kudin man fetur da N5.

Hukumar kudin titi wato National Road Fund,idan aka zantar da dokan samar da ita, zata zama wata kafa na amsan haraji daga hannun masu amfani da hanyar mota domin samun kudin kula da hanyoyin Najeriya lokacin bayan lokaci.

KU KARANTA: Wajibi ne Babachir ya tafi- Sanatoci

Jaridar DailyTrust ta bada rahoton cewa Karin N5 din na daga cikin shawarwarin da kwamitin ta baiwa majalisa karkashin jagorancin Toby Okechukwu.

Game da rahoton tace: “Kudin harajin N5 ga lita zai hau akan kowani man fetur da aka saya ko man gas da aka shigo da shi Najeriya ko kuma aka tace cikin Najeriya."

Kana kwamitin ta bada shawaran cewa a samar da wasu hanyoyin amsan haraji irinsu kudin kofa wato Toll gate, kudin motar da ke shigowa daga wata kasa, kudin jiha da jiha, da kuma kudin motar da aka shigo da ita cikin kasa.

Amma jami’ar samar da manufofi da dabaru wato National Institute for Policy and Strategic Studies (NIPSS) sunyi hannun riga da wannan shawara na Karin N5.

A bangare guda kuma, hukumar National Union of Petroleum and Natural Gas Workers (NUPENG) da Petroleum and Natural Gas Senior Staff Association (PENGASSAN) sunyi gargadi akan wani Karin kudin man fetu saboda mawuyacin halin da yan Najeriya ke ciki.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel