Obama ya caccaki Trump kan hana Musulmai shiga Amurka

Obama ya caccaki Trump kan hana Musulmai shiga Amurka

- Tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama yayi magana kan hana musulmai shiga Amurka da Donald Trump yayi

- Trump ya sanya dokar hana kasashen musulunci guda bakwai daga shiga kasar Amurka

- A halin yanzu tsohon shugaban kasar na jin dadi cewan Amurkawa sun tsaya don yin zanga-zanga ga dakatarwan

Obama ya caccaki Trump kan hana Musulmai shiga Amurka

Obama ya caccaki Trump kan hana Musulmai shiga Amurka

A ranar Litinin, 30 ga watan Janairu, tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya caccaki shugaban kasa Donald Trump kan hana kasashen Musulmai guda bakwai shiga Amurka.

A ranar Juma’a Trump ya dakatar da kasashen musulmai guda bakwai daga shiga kasar Amurka na tsawon kwanaki 90 da kuma dakatar da yan gudun hijira.

KU KARANTA KUMA: Hukumar Kwastam sun kama mutane 3 kan bindigogi 661 da aka cafke a jihar Lagas (HOTUNA)

Hukumar kula da shige da fice ta kasar Amurka ta komar da musulmai da dama daga filin jirgin Amurka kuma yan kaka gidan Amurka sun fara korafi game da masoyansu da aka kulle a wajen kasar sakamakon umurnin shugaban kasa Trump.

Jawabin Obama: "Shugaban kasa Obama ya ji dadin zanga-zangar da ake yi domin tilasta wa Trump ya janye matakin da ya dauka.

Ya kara da cewa Mista Obama na kyamar nunawa mutane wariya saboda imaninsu ko addininsu.

A cewarsa, zanga-zangar da mutane ke yi ta nuna cewa Amurkawa ba za su bari a gurbata mulkin dimokradiyya ba."

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel